Hukumar Sojoji sun kori sojoji biyu bisa laifin kashe Malamin addinin Musulunci da suka yi a Yobe


Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji biyu bisa laifin kashe wani Malamin addinin Islama , Sheikh Goni Aisami Gashua, a jihar Yobe. Shafin labarai na isyaku.com ya samo
.

Sojojin da aka kora sun hada da Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon

Mukaddashin Kwamandan da ke kula da bataliya ta 241 Reece dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, wanda ya tabbatar wa manema labarai haka, ya ce kwamitin binciken hadin gwiwa da aka kafa tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, ta same su da laifin kisan kai. Ya ce an sallami sojojin biyu ne bisa tuhume-tuhume biyu na rashin gudanar da ayyuka da kuma nuna kyama ga horon aikinsu.


Laftanar Kanar Osabo ya kara da cewa za a mika sojojin da aka kora a hannun ‘yan sanda a Damaturu domin gurfanar da su a gaban kotu.

ISYAKU.com ya ruwaito  cewa Malamin yana tafiya ne daga Gashua zuwa Kano lokacin da jami’an tsaron da ya taimaka masu ya rage masu hanya a motarsa suka kashe shi a Jajimaji da ke tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN