NBC ta soke lasisin Ray Power FM, Silverbird TV, da sauran tashoshi 50, duba wasu sunayeHukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta kwace lasisin gidan rediyon AIT/Ray Power FM (DAAR Communication L.td., Silverbird TV Network da wasu gidajen rediyo 50 kan bashin Naira biliyan 2.6. shafin isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa babban Daraktan NBC, Malam Balarabe Ilelah, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja, ya ba da umarnin rufe tashoshin da abin ya shafa nan da sa’o’i 24 masu zuwa.

Ilelah ya umurci ofisoshin NBC na kasa baki daya da su hada kai da jami'an tsaro domin tabbatar da bin ka'ida cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa, a watan Mayun 2022, hukumar ta buga a cikin jaridun kasar nan, jerin sunayen masu lasisin da ke bin NBC bashin, ta ba su sati biyu su sabunta lasisin su kuma su biya basussukan da ake bin su, ko kuma su yi la’akari da soke lasisin su, kuma cire masu mitocin watsa shirye-shiryensu.

“Watani uku bayan fitowar wasu masu lasisin har yanzu ba su biya basussukan da ake bin su ba, wanda ya sabawa dokar NBC Act CAP N11, dokokin Tarayyar Najeriya, 2004, musamman sashe na 10 (a) na jaddawali na uku na dokar.

” Dangane da wannan ci gaba, ci gaba da gudanar da ayyukan tashoshin ya saba wa doka kuma ya zama barazana ga tsaron kasa.

“Saboda haka, bayan an yi nazari sosai, Hukumar NBC ta sanar da soke lasisin tashoshin da ba a tantance su ba tare da ba su sa’o’i 24 su rufe ayyukansu,” inji shi.

Shugaban ya ce sauran tashoshin da abin ya shafa sun hada da Zuma FM, Suleja, jihar Neja, Bomay Broadcasting Service L.td, Kogi, Kwara, Niger, Gombe, Lagos, Osun, Ogun, Ondo da Rivers.

Ya jera wasu tashoshin da suka hada da; Katsina Broadcasting Corporation, Kaduna State Broadcasting Corporation, Jigawa Broadcasting Corporation, Kebbi State Broadcasting Corporation, Zamfara State Broadcasting Corporation da Yobe State Broadcasting Corporation.

Hakazalika, Ilelah ya ce gidajen yada labarai na jihar Imo, Anambara, Cross River, Bayelsa, Borno, Crowther FM Abuja na daga cikin tashoshin da abin ya shafa.

Ya bukaci duk gidajen yada labarai da ba su sabunta lasisin su ba a halin yanzu da su yi hakan nan da kwanaki 30 masu zuwa don kaucewa takunkumi.

Ya kuma yi kira ga daukacin gidan talbijin na Internet Protocol da sauran gidajen yada labarai da ke yawo a yanar gizo da su yi rajista da hukumar domin kaucewa yanke alaka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN