Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle ya kubutar da dan sanda daga hannun masu garkuwa da mutane


Gwamna Bello Matawalle na Zamfara a ranar Laraba ya tabbatar da sako DSP Usman Ali, jami’in kula da ofishin ‘yan sandan Magami da ke Gusau daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan, Jamilu Birnin-Magaji ya fitar.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da DSP Ali a ranar 12 ga watan Agusta a hanyar Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara.

Sai dai Gwamnan ya tabbatar da sakin wanda aka yi garkuwa da shi ne ta hanyar kokarin da jami’an tsaro suka yi a jihar inda suka gabatar da shi ga Gwamna a gidan Gwamnatin Gusau, ba tare da an ji masa rauni ba.

Matawalle a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in, ya bayyana gamsuwa da matakan da Gwamnati ta dauka na magance ‘yan fashi da garkuwa da mutane a jihar.

Ya taya wanda aka zalunta murnar samun ‘yancinsa tare da addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalar ‘yan fashi da sauran laifuka.

Ali ya godewa gwamnan da duk wadanda suka taka rawa wajen kwato masa ‘yan bindiga

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN