Yan sanda sun kai samame matattaran bata-gari a Abuja, sun fatattake su sun kona wurin kurmus


Tawagan yan sanda da guda biyar a birnin tarayya Abuja, a daren ranar Laraba sun kona wani mabuyar yan ta'adda a Dawaki Zone 7 na Abuja bayan bata garin da ke zama a wurin sun tsere bayan hango yan sandan

The Punch ta rahoto cewa bata gari da ke adabar mjtanen Dawaki da Dutsen Alhaji a Abuje ne ke zama a wurin.

Wani mazaunin unguwar wanda ya nemi a boya sunansa ya ce mabuyar ne matattaran bata gari, yana mai cewa mutanen gari suna tsoron bi ta wurin musamman da dare.

Jami'an yan sanda daga Dawaki, Zuba, Kubwa, Bwari da Dutse Alhaji ne suka kai harin karkashin jagorancin DPO SP Ali Johnson.

Wani dan sanda, wanda ya nemi a boye sunansa ya ce an kona wurin ne domin hana bata gari taruwa kuma su mayar da wurin sansanin masu laifi.

Ya ce, "Bata garin sun cika wandunansu da iska bayan sun hango mu. Hakan yasa ba mu da wata zabi sai kona wurin."

Kakakin yan sandan Abuja ta yi karin haske

Da ta ke tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun yan sanda na Abuja, Josephine Adeh, ta ce atisayen na cikin kokarin da rundunar ke yi na kawar da laifuka a birnin tarayya.

Adeh ta ce, "Muna lalata duk wani matattaran bata gari da nufin fatattakar masu laifi daga birnin tarayya Abuja.

"Mun kai samame wurin domin yana iya sauyawa ya zama matattaran masu laifi."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN