Kebbi za ta gudanar da wani abin alheri kan ayyukan lafiya a mataki na farko - Bagudu

Kebbi za ta bunkasa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko - Bagudu


Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yi alkawarin bunkasa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a jihar. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Bagudu, wanda ya samu wakilcin SSG, Babale Umar Yauri, ya yi jawabi a ranar Asabar, a Birnin Kebbi, lokacin da ya karbi tawagar wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Chigari Foundation’ a gidan Gwamnati dake Birnin Kebbi.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin tunkarar sama zuwa kasa wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya da hada-hadar masu ruwa da tsaki kan harkar lafiya a jihar.

Bagudu ya kuma sha alwashin rage asarar rayuka da ba dole ba a sakamakon cututtuka, wanda galibi ana yin rigakafinsu.

Gwamnatin jihar ta samu nasarar aikin kiwon lafiya a matakin farko sama da kashi 82 cikin dari a fadin jihar, in ji shi.

 “Gwamnatin Jiha za ta samar da aÆ™alla guda É—aya mai É—orewa, ingantattun kayan aikin PHC a duk mazabu 225.

“Ya zuwa yanzu, Gwamnatin ta gyara PHC 140, yayin da 36 ke ci gaba da aiki.

“Hakazalika, za a dauki kwararrun ma’aikatan lafiya 850 kafin karshen wannan gwamnati, domin cike gibin da ake samu.

' Hakazalika, ana gudanar da wani asusu na jujjuya magunguna, da kuma kafa hukumar inshorar lafiya ta jiha".

Ya yabawa gidauniyar bisa kokarin da take yi na samar da ayyukan ceton rai musamman na rigakafi.

Kwamishinan lafiya na jihar, Hon Jafar Mohammed, ya yabawa gidauniyar bisa gagarumin kokarin da take yi na kara yawan allurar rigakafi a jihar da sauran sassan kasar nan.

Shugaban tawagar, Farfesa Ali Pate, tsohon Ministan lafiya, ya ce sun kai ziyarar ne domin tuntubar masu ruwa da tsaki a kan kokarin da ake yi na tsara dabarun yin alluran rigakafi da kuma kara kaimi.

A cewar Pate, an dauki wannan mataki ne da nufin inganta harkokin kiwon lafiya a kasar, da kuma rage illar cututtuka masu yaduwa.

Tawagar gidauniyar Chigari ta samu jagorancin Farfesa Ali Muhammad Pate da Dokta Muyi Aina da babban jami’in gudanarwa na SOLINA da Alhaji Aminu Inuwa Muhammad shugaban gidauniyar Sultan da Dokta Usman Abubakar Gwandu.

6/8/2022

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN