Rikicin PDP: Atiku da Gwamna Wike sun cimma wata matsaya, duba ka gani


Sakamakon taro tsakanin É—an takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, da gwamna Nyesom Wike na Ribas, an kafa wani kwamitin mutum 14 daaa zai tattauna kuma ya ba shawarwari wanda jiga-jigan biyu zasu diba. Legit.ng ta ruwaito.

Wata babbar majiya mai alaƙa da cigaban ce ta sanar da jaridar Vanguard ranar Lahadi cewa ba'a bayyana wa duniya kwamitin bane saboda har yanzu akwai mambobin kwamitin da ba'a sanar da su ba.

Majiyar wacce ta yi jawabi da sharaÉ—in boye bayananta saboda wasu dalilai ta ce kwamitin zai fara fara aikin da aka É—ora masa nan take.

Babbar jam'iyyar hamayya watau PDP ta afƙa cikin rikici tun lokacin da Atiku Abubakar ya zaɓi gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin ɗan takarar mataimaki a zaɓen 2023.

Sai dai wannan zaɓin ya saɓa wa tunanin wasu masu faɗa aji na PDP da ke tunankn Wike ya fi dacewa da matsayin bayan ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani wanda aka ayyana Atiku a matsayin ɗan takara.

Mako biyu da suke wuce, Atiku da gwamna Wike sun yi musayat zafafan kalamai kan zaɓen mataimaki, lamarin da ya sa kwamitin amintattu suka shiga tsakani.

Mun samu cigaba cikin awanni 24 da suke wuce bayan ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da gwamna Nyesom Wike sun gana. Taron ya ba maƙiyan PDP mamaki," inji majiyar.

Shin wani bangare ya gindaya sharudda ne?

Da aka tambaye shi ko an gindaya wasu sharuɗɗa a zaman, majiyar ta ƙara da cewa:

"Zancen kafa wasu sharuÉ—É—a be ta so lokacin mutanen biyu suka jingine sabanin da ke tsakanin su, suka yi magana da juna. Duk shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar za'a duba su kuma a É—auki mataki."

Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan rikicin, kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya bayyana kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba za'a kawo ƙarshen komai

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN