Da duminsa: Hukumar shari'a ta jihar Kogi ta bankado ma'aikatan bogi guda 268


Ma’aikatar shari’a ta jihar Kogi ta bankado ma’aikatan bogi 268 da ke karbar albashin babbar kotun jihar.  Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Mukaddashin Alkalin Alkalan jihar, Mai shari’a Josiah Majebi, ya kafa Kwamitin tantance ma’aikatan da zai binciki jerin sunayen manyan kotuna. 

Shugaban kwamitin, Mai shari’a Mohammed Etsu Umar, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, yayin da yake gabatar da rahoton ga mukaddashin Alkalin Alkalai, a Lokoja. 

Kwamitin ya kuma ba da shawarar a dakatar da duk wasu nade-naden ‘ba bisa ka’ida ba’ a ma’aikatar shari’a ta jihar Kogi tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Yuni 2022. 

Mai shari’a Umar ya ce rashin sanin ya kamata ya haifar da karuwar yawan wadanda ake yiwa ma’aikata karin girma, wanda ya nuna an samu karin kashi 40 cikin 100 na kudin ma’aikata. 

“Bayan an yi nazari sosai kan sunayen sabbin ma’aikatan da aka dauka daga watan Janairu 2021 zuwa Yuni 2022, da jerin sunayen ma’aikatan da kuma lissafin albashi, an gano cewa ba a iya samun wasu sunayen da ke cikin takardar albashin a cikin jerin sunayen ma’aikatan na Kotuna, da sauran sassa ba,” inji shi.

“Saboda haka, hakan ya nuna cewa duk da sunayensu na cikin takardar biyan albashi, ba su da gidajen kwana kuma ba sa aiki a ko’ina a ofisoshin hukumar,” in ji shi. 

A cikin jawabinsa, CJ ya ce aikin zai kasance ci gaba da aiki don tabbatar da bin tsari da kuma himma wajen daukar ma’aikata da gudanarwa. 

Ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin kwamitin ba tare da bata lokaci ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN