Jirgin yaƙin sojoji ya hallaka kasurgumin dan bindiga, Alhaji Shanono, da wasu 17 a Kaduna


Rundunar Sojojin saman Najeriya (NAF) ta halaka ƙasurgumin shugaban yan ta'adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaƙansa guda 17 a jihar Kaduna.

Alhaji Shanono da yan tawagarsa sun bakunci lahira ne a wurin wani taro a Ukambo, wani ƙauye mai nisan kilomita 131 daga Kaduna lokacin da jirgin rundunar Operation Whirl Punch ya musu luguden wuta ranar Talata.

Wani babban Jami'i a hukumar sojin saman Najeriya ya shaida wa Leadership cewa sama da bindigu 30, Babura 20 luguden wuta ya ragargaza yayin da wasu mutum 26 da ke tsare hannun yan ta'addan suka kubuta.

Wannan na samame na ɗaya daga cikim nasarorin da hukumar doji ta samu a yankin, inda Jami'in ya bayyana cewa:

"Samamen da jirgin NAF ya kai ya yi sanadin sheƙe yan ta'adda da dama tare da rugurguza maɓoyarsu. Ɗaya daga cikin irin waɗan nan farmakin da Jirgi ya kai jiya 9 ga watan Agusta ya halaka sanannen shugaban yan ta'adda a Kaduna."

"Bayan samun bayanan sirri a jiya cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Alhaji Shanono, ya shirya taro da mayakansa a kauyen Ukambo kilomita 131 daga Kaduna, nan take Jirgin Operation Whirl Punch ya tashi zuws wurin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN