Akanta Janar da aka dakatar, Ahmed Idris yana neman yin sulhu da Lauyoyin EFCC


Ahmed Idris wanda aka dakatar daga matsayin babban akawun gwamnatin tarayya, yana neman ya yi sulhu da hukumar EFCC da ke kararsa.

Rahoton The Cable na ranar Laraba, 10 ga watan Agusta 2022, yace wanda ake kara ya fara shirin ganin yadda za a janye tuhumar da ake yi masu a kotu.

Da aka koma kotu a jiya da rana, sai Lauyan da ya tsayawa EFCC, Rotimi Jacobs ya shaidawa Alkali, Idris da sauran wanda ake zargi sun tuntube shi.

Rotimi Jacobs yake cewa wadanda ake karar suna neman haduwa da shi ne saboda a janye karar.

Abin da Lauya ya fadawa kotu

“Mai shari’a, wadanda ake tuhuma sun aiko mani da wani mutum, suna so mu sasanta, kuma suna neman ganawa da ni,”

“Saboda yanayin aikinmu, dole ne muyi komai keke-da-keke cikin gaskiya.”

- Rotimi Jacobs

Ayi komai a gaban Lauyoyi

Vanguard ta rahoto Jacobs yana cewa tun da sashe na 270 na dokar shari’a ta kasa ta amince da irin wannan tsari, ya bukaci Idris su zo da layoyinsu.

Shi ma Lauyan na EFCC ya yi alkawarin gayyato masu bincike daga bangarensa wajen ganawar. A karshe dai har zuwa jiya, hakan ba ta yiwu ba.

Jacobs yake cewa daga baya Lauyoyin Idris sun same shi a ofishinsa, inda suka nuna fushinsu saboda an ware su, a dalilin hakan aka fasa wannan zama.

Sulhu a wajen kotu

A kotu akwai tsarin da ake bi ta yadda za a cin ma matsaya tsakanin wanda ake kara da bangaren wanda ya shigar da kara, ta yadda za a daina shari’ar.

Kotu ta kan amince da wannan tsari idan har Lauyoyi sun gamsu maganar ta bar teburin Alkali. A irin wannan, kowa bai samu cikakken abin da yake so.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN