Asirin sabon Ango ya tonu bayan ya bar Amaryarsa a wajen bikin aure ya je wajen wata Karuwa domin yin lalata da ita


Asirin wani sabon Ango ya tonu bayan ya yi yunkurin yin lalata da wata Karuwa lokacin da suke cikin hutun amarci da Amaryarsa. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Paul Turovsky, mai shekaru 34, yana hutun Amarci ne a gundumar Hillsborough da ke jihar Florida na kasar Amurka, inda ya zarce da sabuwar matarsa ​​don hutawa.

Rahotannin sun bayyana cewa, ya samu wani talla, wadda matar ta tallata kanta na neman masu son yin jima'i da ita su biya ta. Sakamakon haka ya je wani wuri da ba a bayyana ba domin saduwa da matar.

An tuhumi mijin da laifin neman Karuwa, kuma zai gurfana a gaban kotu a karshen wannan shekarar.

Ba a san abin da ya faru da sabuwar matarsa ​​ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN