Wasu ‘yan bindiga sun sare hannaye biyu na wani Malam Bisallah a kauyen Wadu Kauran, cikin karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, amma a cewar shaidu, ‘yan fashin sun far wa kauyen inda suka yi awon gaba da shanu, tumaki da sauran dabbobi.
Da ‘yan bindigar suka dawo daga baya suka tafi da kaji, Malam Bisallah ya kasa jurewa wannan ta’asa, ya fuskanci su. Ya ce masu:
"Me kuke so? Wane irin ciwo kuke haddasa mana?" sai ya ce wa ‘yan fashi.” Me ya sa kuke yi mana haka, wane laifi muka yi muku?
Sakamakon haka barayin suka kama shi suka sare masa hannayensa. An kuma tattaro cewa sun kashe wasu mutanen kauyen yayin harin.
Yanzu haka dai wanda aka sare wa hannuwa yana kwance a babban asibitin Kaura Namoda yana jinya.