2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP


Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ganawar da Atiku Abubakar ya yi da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ta gaza kawo wani sauyi a rikicin da ke tsakaninsu
.

A cewar rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da gwamnan a gaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin.

An ce tsohon ministan yada labarai da al’adu, Farfesa Jerry Gana ne ya shirya taron a gidansa.

A wani taro da mambobin BoT na PDP a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, Atiku ya bayyana cewa PDP za ta iya lashe zaben badi ba tare da kuri’un jihar Ribas ba.

Ya ce babu wani abin fargaba idan Wike bai so ya goyi bayansa ba a yakin neman zabensa.

Cike da kwarin gwiwa, Atiku ya tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ma bai ci jihar Ribas ba, ya dogara ne da kuri’u daga jihohin Legas, Kano da sauran jihohin da ya kamata ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

Ya kuma ce PDP ta shiga taskun rikici ne saboda Wike ya sanya batun kudi a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar.

Mutanen Wike na neman a sake fasalin PDP

A halin da ake ciki, masu biyayya ga Wike sun yi kira da a sake fasalin shugabancin PDP don kara samun karbuwa a kudu, suna masu cewa jam'iyyar, kamar yadda take a yanzu, ta fi karfi a Arewa.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sansanin gwamnan ya koka da yadda tsarin jam’iyyar ya karkata zuwa ga ‘yan Arewa, inda ya jaddada cewa duk wani shirin sulhu tsakanin Atiku da Wike dole ne ya tattauna mafita ga hakan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN