Hotuna: Kyawawan jaruman fim mata 3 da suka auri zakarun Super Eagle..isyaku.com


Soyayya gamon jini ce inji Hausawa. Zakaru kuma 'yan wasan Super Eagles sukan gangara daga duniyar wasanni zuwa daukan abokan rayuwa kyawawa wadanda suka dace dasu kuma su gina iyali. Jaridar legit ta wallafa.

Wasu daga cikin kwararrun 'yan kwallon kafa sun ci karo ne da soyayya a masana'antun fina-finai inda suka auri kyawawan jarumai.

Ga hotuna da bayanin jarumai mata na fim da suka sace zukatan 'yan kwallon kafa kuma suka shige aka ciki:

1. Kalu Uche and Stephanie Oforka

Tsohuwar sarauniyar kyau kuma jarumar fim, Stephanie Oforka, ta yi shuhura a shekarar 2008 yayin da ta zama wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a Najeriya.

A 2011, ta auri tsohon zakaran kwallon kafa na Super Eagles, Kalu Uche wanda yayi wa Najeriya wasa tsakanin 2003 zuwa 2012.


2. Olayinka Peters da Yetunde Barnabas

Zakaran kwallon kafa na Slavia Prague, Olayinka, shima kwararren 'dan wasan kwallon kafa na Super Eagles ne wanda a yanzu haka yake auren jarumar fina-finan kudancin Najeriya.

A halin yanzu, zakaran kwallon kafan yana auren fitacciyar jaruma Yetunde Barnabas.

Kyawawan ma'auratan sun yi aure a watan Maris din 2021. Jarumar ta ci gasar kyau ta Najeriya a 2017 kuma an nada ta jakadiyar yawon bude ido a Najeriya a 2019.

Jarumar ta yi suna da fice ne a rawar da ta taka matsayin Miss Pepeye a shirin Papa Ajasco.


3. Shehu Abdullahi da Naja'atu Muhammad

Shehu fitaccen zakaran wasan kwallon kafa na Super Eagles wanda ke auren jarumar Kannywood.

An daura auren masoyan juna Naja'atu Muhammad da Shehu Abdullahi a ranar 18 ga watan Yunin 2021, kwanaki kasan kafin auren Yetunde Barnabas.

Ahmed Musa, kyaftin din Super Eagles ya samu halartar daurin auren.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN