Wasu bata gari sun kai hari hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Agwa a karamar hukumar Oguta, Jihar Imo a daren ranar Juma'a sun kashe yan sanda hudu, The Punvh ta rahoto.
Maharan sun kuma kone wasu motocci na rundunar har ma da na DPO
Kuma yan bindigan sun kutsa gidan wani mutum mai suna Ejike sun bindige shi tare da matarsa har lahira.
Hakan ya janyo tashin hankali a unguwar a yayin da yan asalin garin da mazauna suka nuna damuwa matuka.
Majiyoyi wadanda ba su so a ambaci sunansu sun bayyana cewa maharan sun taho ne misalin karfe 10 zuwa 11 na dare a motocci uku.
A cewar majiyoyin, yan bindigan sun taho ne cikin tipper daya da wasu motoccin kirar sienna guda biyu suka afka wa ofishin yan sandan.
Cikin yan sandan da aka kashe, biyu maza ne sannan sauran biyun mata kuma an cinna wa gawarsu wuta.
A cewar majiya, daya daga cikin yan sandan da aka kashe sabon ma'aikaci ne, satinsa biyu da fara aiki.
Daya cikin motoccin da aka kona ta DPO ce.
Wata majiya daga rundunar yan sanda ta ce an turo wasu yan sandan daga wani ofishi su tsare wurin yayin da ake jiran zuwan Kwamishinan yan sanda, Muhammad Berde, Daily Trust ta rahoto.
Mai magana da yawun yan sanda na jihar, CSP Mike Abattam bai riga ya ce komai kan lamarin ba domin kirar da aka yi masa ba su shiga ba.