Jerin Sanatocin APC da suke goyon bayan shirin tsige shugaba Buhari


A ranar Laraba, 27 ga watan Yuli ne Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP suka gudanar da zanga-zanga bayan da shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya hana Sanata Philip Aduda tattauna matsalar rashin tsaro. Shafin Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa mafi yawan ‘yan Majalisar sun amince cewa a baiwa Buhari wa’adin makonni shida domin ya gyara rashin tsaro ko kuma a tsige shi.

Aduda ya ce akwai bukatar a mika wa shugaban kasa sanarwar a hukumance, amma Lawan ya ki amincewa da hakan. .

Bayan ficewa daga zauren Majalisar, Sanatocin sun baiwa shugaban kasar wa'adin makonni shida domin ya magance matsalar rashin tsaro a kasar ko kuma a iya tsige shi.

Kakakin shugaban kasar ya mayar da martani

Da yake mayar da martani kan lamarin, mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce 'yan Majalisar na bata lokaci ne kawai, yana mai cewa ba za su iya aiwatar da barazanarsu ba.

Ya bayyana barazanar a matsayin fanko wanda ba za a iya aiwatar da shi ba.

“Gaskiyar magana ita ce ‘yan tsiraru za su fadi ra’ayinsu yayin da masu rinjaye za su kasance da yadda suke so. Idan kun san yadda ake tafiyar da Majalisun kasa da na Majalisar Dattawa, wadanda suka yi magana a yau tsiraru ne,” in ji Adesina.

Sai dai kuma sabanin kalaman Adesina na cewa ‘yan Majalisar adawa ne kawai ke barazanar tsige shi, akalla gwamnonin APC biyu ne suka fito fili suka goyi bayan matakin.

Sanata Elisha Abbo

Sanata Elisha Abbo, dan Majalisar wakilai na tarayya daga jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa, ya yi kira ga a tsige shugaba Buhari.

Abbo ya bayyana matsayar sa kan kiran da aka yi na tsige shugaban kasa a taron shugabannin Kiristocin Arewa da aka yi a Abuja ranar Juma’a 29 ga watan Yuli.

Sanatan ya shaidawa manema labarai cewa dalilinsa na goyan bayan kiran yana da nasaba da rashin iya jurewa da kuma tabarbarewar yanayin tsaro da Najeriya ke ciki.

Adamu Bulkachuwa

Wani Sanata a jam’iyyar APC mai mulki, Adamu Bulkachuwa, ya goyi bayan shirin tsige shugaba Buhari saboda tabarbarewar tsaro a kasar.

Bulkachuwa mai wakiltar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dokoki ta kasa ya ce shi da takwarorinsa sun yi kokari ta hanyoyi da dama don taimakawa shugaban kasar wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar amma abin ya ci tura.

"Mu a Majalisa, mun gwada duk abin da ke cikin ikonmu, sai dai abu ya buwaya," in ji dan Majalisar da ransa ya baci.

Bulkachuwa ya ce barazanar da Sanatocin adawa ke yi na tsige Shugaba Buhari ita ce zabi na karshe da ya rage wa ‘yan Majalisar.

Da aka tambaye shi ko Sanatocin APC na cikin wadanda suka yi kira da a tsige shugaba Buhari, ya mayar da martani kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN