Kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.
Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.
Jaridar ta ambaci majiya na cewa mamacin ya hallarci jana'iza a Damaturu babban birnin Jihar Yobe a yammacin ranar Talata, kafin ya kama hanyar zuwa Jihar Kano.
Za a yi jana'izarsa a ranar Laraba a Damaturu domin an koma da gawarsa Yobe babban birnin jihar Yobe a daren ranar Talata, Daily Indepedent ita ma ta rahoto.
Ya rasu ya bar mata byu da yara.