Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II sun gana a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar Litinin 1 ga watan Agusta. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na farko da za a ga Gwamna da tsohon Sarki tare tun bayan da Ganduje ya tsige Sanusi a shekarar 2020.
A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ya dauki ganawar tasu, an ga tsohon sarki da Ganduje suna gaisawa a wani dakin shakatawa da ke filin jirgin sama yayin da Gwamnan ke murmushi.
Kalli bidiyon a kasa.............