Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin sun yi garkuwa da dan makwabcinsu dan shekara 13 a karamar hukumar Tafa da ke jihar. Kafar labarai na yanar gizo Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.
Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, ya ce an kama wadanda ake zargin Usman Sabiu da Nafiu Umar ne biyo bayan rahoton da rundunar ta samu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli kan yaron da ya bata mai suna Yasir Salisu.
A cewar PPRO, wadanda ake zargin sun sace yaron ne da nufin karbar Naira 100,000 daga hannun mahaifinsa.
Da aka yi masa tambayoyi, Sabiu ya amsa cewa sun shake yaron har lahira kuma sun binne shi a wani kabari mara zurfi saboda bai iya samar da lambar wayar salula na mahaifinsa da za su yi amfani da shi domin neman kudin fansa ba kuma ya gane su.