Yan bindiga sun yanka jariri, sun kashe mutum 10 a Taraba, Filato


A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Joro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, inda suka kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu shida. Shafin labarai na Isyaku News online (isyaku.com) ya samo.

Akalla mutane bakwai ne kuma wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka kashe a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Mazauna kauyen Joro Manu sun ce maharan sun zo ne a kan babura da misalin karfe biyu na rana inda suka harbe duk wanda suka gani.

Wasu mazauna unguwar Umar Saidu da Abdullahi Mohammed sun shaida wa wakilinmu cewa mutane na gudun kada a kashe su ko kuma a yi garkuwa da su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Gambo Kwache, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin ‘yan sandan ya ce, “Muna kan lamarin. Mun tura jami'an mu yankin domin zakulo maharan.”

Tsohon shugaban karamar hukumar Gassol, Musa Chul, a shekarar da ta gabata ne ya koka kan yadda ‘yan ta’adda suka sake haduwa a dazuzzukan yankin karamar hukumar.

Sai dai kashe-kashen da aka yi a garin Jos ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan wasu mutane 18 suka rasa rayukansu a wani rikici da ya barke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan kungiyar ‘yan banga a yankin karamar hukumar Wase da ke jihar Filato.

Sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Mooulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da kisan na baya bayan nan a ranar Litinin.

Ya ce harin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na dare a unguwar Danda Chugwi da ke yankin karamar hukumar.

Tengwong ya ce, “An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a yankin Danda Chugwi bayan wani hari da wasu ‘yan bindigar Fulani suka kai.

“Wasu kuma wadanda suka samu munanan raunukan harbin bindiga, an kai su Asibitin Kirista na Vom domin a kula da lafiyarsu cikin gaggawa.”

An bayyana cewa a cikin wadanda suka jikkata har da wani jariri dan wata hudu da ‘yan bindigar suka yanke masa hannu.

Tengwong ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka kashe sun hada da Pam Dawho mai shekaru 59; Nvou Gyang, mai shekaru 43; Jah Pam, 50; Ruth Bot, 16; Chundung Gyang, 9; Mercy Gyang,12; da Benjamin Gyang. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN