Dara ta ci gida: Kofur na yan sanda ya naushe hafsan yan sanda lokacin gardama a kan titi a bainar jama'a, duba daliliA ranar Asabar 6 ga watan Agusta ne wani jami’in ‘yan sanda ya afkawa wani babban jami’in dan sanda a Simbiat Abiola Way, Ikeja, jihar Legas bayan wata gardama da ta barke a tsakaninsu. Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kofur din da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya fuskanci babban jami’in, wanda aka bayyana sunansa da Supol Edgar, bisa zarginsa da haddasa cunkoso a mahadar hanyar Awolowo.

An ruwaito cewa kofur ya yi wa Edgar naushi ne, ba tare da sanin cewa shi dan sanda ne da ke zaune a wani bariki da ke kusa da wurin ba

Babban jami’in ‘yan sandan ya je ya kira abokan aikinsa da ke cikin bariki, inda suka fito suka dunkule dan sandan suka tafi da shi cikin harabar su. 

Wani ganau da ya bayyana sunansa Stanley bisa dalilan tsaro, ya ce wani direba adaidaita sahu ne ya haddasa matsalar, wanda ya yi kokarin bi ta wasu motocin da ke mahadar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN