Da duminsa: 'Yan sanda sun kori kofur Opeyemi Kadiri saboda binciken wayar wani matafiyi (hotuna/bidiyo)


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori wani ‘dan sandan Najeriya mai lamba 509745 Kofur Opeyemi Kadiri da ke aiki a hedikwatar Dolphin reshen jihar Legas bisa laifin aikata mugun aiki, rashin bin doka da oda, da kuma cin zarafi kan jama’a da aka dauka a wani faifan bidiyo a ranar 3 ga Agusta, 2022. Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Korarriyar jami’in da ya shiga rundunar a ranar 6 ga watan Disamba, 2016, an kama shi ne yana binciken wayar wani matafi a gefen hanya sabanin umarnin babban sufeton ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, kan haka. Haka kuma ya ci zarafin matafiyin da ya yi yunkurin kawo masa odar. Korar tasa ta fara aiki daga yau 12 ga watan Agusta, 2022.

Wata sanarwa da CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta yi kira ga hafsoshi da jami’an rundunar da su ci gaba da kwarewa da wayewa ga jama’a wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada. Hakazalika rundunar ta yi kira ga jama’a da su tabbatar da gudanar da ayyukan da suka dace a duk wata ganawa da jami’an ‘yan sanda domin kaucewa munanan laifuka da za a iya gurfanar da su a gaban kuliya.

Latsa kasa ka kalli bidiyo...

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN