An caka wa Salman Rushdie wuka sau 15, mutumin da ya rubuta littafin "Satanic verses" na batanci ga Annabi da Musulunci


An caka wa Marubucin littafai Salman Rushdie wuka yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taro a birnin New York na kasar Amurka. An garzaya da shi asibiti a jirgi mai saukar Angulu nan take. Shafin la arai na Isyaku News isyaku.com ya samo

Dan shekara 75,Dan asalin kasar India, Marubucin ya fito zai gabatar da jawabi ne a taron CHQ 2022 a Chautauqua, kusa da Buffalo, ranar Juma'a 12 ga watan Agusta, kwatsam sai wani mutum ya fito ta baya ya caka wa Salman Rushdie wuka da wani shaidun gani da ido ya ce kusan say 10 zuwa 15.

An kama mutumin yayin da cinkoson jama'a da suka ruga domin taimaka wa Rushdie suka hana mutumin wucewa kafin Yan sanda su ka zo suka kama shi.

Gwamna Kathy Hochul ta bayyana harin a matsayin "abin takaici" ta kuma tabbatar da cewa Rusdie yana raye yana samun kulawan da ya dace a wani Asibiti.

Wannan lamarin na faruwa ne shekara 33 bayan Marubucin ya fuskanci barazanar kisa sakamakon wani littafi da ya rubuta mai suna "Satanic verses" wanda ke cike  da batanci ga Annabi Muhammadu da addinin Musulunci.

Lamari da ya ja tofin Allah tsine daga kasashen Musulmi a Duniya a 1988 Kuma ya jawo zanga-zanga a kasar Britaniya tare da kone littafin.

Daga bisani zanga-zanga ya barke a wasu kasashen Musulmi na Duniya, lamari da ya jawo mutuwar mutane 60 tare da raunata daruruwan jama'a .

Kasar Pakistan ta haramta littafin, yayin da shugaban kasar Iran na waccan lokaci Ayatullah Khomeini, a watan Fabrairu 1989, ya bayar da Fatawar kisa ga Salman Rushdie tare da sa ladar Dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sakamakon haka kasar Britaniya ta samar masa da tsattsaurar tsaro a fadin kasarta.

A shekara ta 2000, Salman Rushdie ya koma kasar Amurka da zama cikin tsatsaurar matakan tsaro kafin faruwar wannan lamari. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN