Hukumar NBC ta ci Aminiya tarar Naira Miliyan 5 saboda tona asirin Yan bindiga


Hukumar Kula da kafafen watsa labarai ta Najeriya, NBC, ta ci gidan watsa labarai na Trust Television Network (Trust TV) tarar Naira miliyan 5 kan bidiyon da ta wallafa mai taken "Nigeria's Banditry: The Inside Story" wanda aka fitar a ranar 5 ga wa

NBC, cikin wasikar da ta aike wa kamfanin mai kwanan watan ranar 3 ga watan Agustan 2022, mai dauke da sa hannun shugabanta, Balarabe Shehu Illela, ta ce an saka tarar ne kan Trust TV saboda wallafa bidiyon wanda ya saba da dokokin NBC.

A cikin sanarwar, mahukunta a ta Media Trust ta ce:

"A halin yanzu muna nazarin matakin da hukumar ta dauka da abin da za mu yi, muna son mu bayyana cewa a matsayin mu na gidan talabijin, mun yi imanin cewa abin da muka yi don amfanin al'umma ne don karin haske kan matsalar yan bindiga da yadda ya ke shafan kasar mu."

“Bidiyon ya nuna tushen rigingimu tsakanin mutane da kuma matsaloli da suka haifar da rikicin makamai da ya zama tubali kan matsalar mutane na jin kai a Najeriya.

“Har ila yau, ta tattara muryoyin kwararru da manyan masu ruwa da tsaki don samar da mafita, ciki har da na Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, Sanata Saidu Mohammed Dansadau, wanda ya fito daga daya daga cikin yankin da suka fi fama da matsalar a Jihar Zamfara."

Sanarwar ta kara da cewa an gabatar da kwararru a cikin bidiyon kamar Farfesa Abubakar Saddique na Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria da Dr Murtala Ahmed Rufai na Jami'ar Usamanu Dan Fodio, wadanda sun dade suna nazari a kan lamarin.

Bidiyon ya kuma bayyana labarai marasa dadi daga mutanen da harin yan bindigan ya shafa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN