An kama wani mutum yana yiwa ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara 12 fyade


An kama wani mutum mai shekaru 42 mai suna DonChris John yana yiwa wata yarinya ‘yar makwabciyarsa mai shekaru 12 fyade a jihar Ebonyi. Shafin labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama (HURIDE) Sampson Oko Nweke, wanda ya bayyana hakan a shafin Facebook, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 6 ga watan Agusta a unguwar Inyere da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa. 

A cewar Mista Nweke, an aiki yarinyar ne zuwa wani aiki, lokacin da wanda ake zargin ya yaudare ta zuwa gidansa tare da yi mata fyade. 

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce yarinyar ta gaya masa cewa su yi wani abu.

"Na ga wata karamar yarinya za ta je wani wuri, diyar (an sakaya sunanta); na kira ta ta zo ta taimake ni ta bare rogo, a lokacin da take taimaka mini in bare rogo, sai ta ce mini tana jin yunwa. Da na shiga ciki na kawo. abincin ta biyo ni, ta ce idan mun ci abincin za mu yi wani abu (yi jima'i) na karba, na danna nononta sai ta fara ihu, na yi mata fyade" kafin masu wucewa suka kewaye gidana." 

A halin da ake ciki, HURIDE tare da taimakon wasu shugabannin kauyen da jami’an tsaro na Ebubeagu, sun tabbatar da cewa an kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda na Achiagu da ke kusa inda za a mika shi yadda ya kamata domin ci gaba da shari’a. An kai yarinyar Abakaliki domin a duba lafiyarta, da yiwuwar jinya da kuma shawarwarin da ta dace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN