An kama wani matashi dan shekara 25 da ya jefe 'ya'yansa 2 da duwatsu har lahira (Hotuna)


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta, ta kama wani matashi dan shekara 25 bisa zargin kashe ‘ya’yansa biyu masu shekaru 3 da 5 a yankin Himikidu da ke karamar hukumar Michika. Shafin isyaku.com ya samo.

Wanda ake zargin mai suna Elisha Tari kuma mazaunin Himikidu da ke karamar hukumar Michika, an ce ya kashe yaran ne da duwatsu da kuma sanduna da ya yi amfani da su wajen dukansu a kai sau da dama. Kakan wadanda abin ya shafa ne ya sanar da faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Michika.

Binciken farko ya nuna cewa mahaifiyar mamacin ta rabu da wanda ake zargin watanni biyu da suka gabata bayan sun samu rashin fahimta. An kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa kasar Kamaru, kuma a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda ana gudanar da bincike don gano dalilin kisan ‘ya’yansa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP SK Akande, ya bayyana alhininsa kan wannan abin bakin ciki da ya faru, ya kuma umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan CID da ya dauki nauyin bincike tare da tabbatar da gurfanar da shi gaban Kotu.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN