Tsohon Gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, zai bayyana sha'awar tsayawa takarar kujerar Sanatan Filato ta tsakiya a jam'iyyar Labour Party (LP). Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.
Dariye, tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, da wasu mutane uku, a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, an sako su daga gidan Yari watanni uku bayan afuwar da Majalisar jihar karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, a ranar 14 ga Afrilu, 2022.
An sako Dariye, wanda zai shafe shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin zamba Naira biliyan 1.126.
bayan kimanin shekaru hudu a gidan yari.
Kamar yadda DailyTrust ta ruwaito, kungiyar LP reshen jihar Filato ta kammala shirye-shiryen karbar tsohon Gwamnan Filato daga Abuja domin karbar fom din takarar Sanata.
Dariye wanda ya taba zama Gwamnan jam’iyyar PDP ya fice daga jam’iyyar. Ya yi takara kuma ya lashe kujerar Sanata a 2011 a jam'iyar LP.
Wani jami’in jam’iyyar Labour da ya nemi a sakaya sunansa ya ce
“Eh, gaskiya ne shi (Dariye) zai tsaya takarar kujerar Sanata. Muna shirye-shiryen zuwan shi daga Abuja domin yin shelar Sanata”.