Zaben Osun: Peter Obi ya magantu kan nasarar Adeleke, ya fadawa mabiyansa mataki na gaba da za su dauka


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya taya Ademola Adeleke, wanda ya lashe zaben Gwamnan Osun da aka kammala murna. Shafin isyaku.com ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa ta hanyar Twitter a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, Obi ya aika da sakon girmamawa da taya murna ga Adeleke kan nasarar da ya samu.

Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma yabawa dan takarar gwamna na jam'iyyar LP da mataimakinsa Rt. Hon Lasun Sulaimon Yusuff da Adeola Adekunle Atanda bisa jajircewarsu a lokacin zaben.

Obi ya bayyana cewa, duk da cewa jam’iyyar ta shafe makonni ne kawai tana fafutukar yaki da wasu tsare-tsare da aka shafe shekaru kusan 20 ana yin su a fadin Najeriya, LP kara bayyana a fadin kasar.

Ya kuma ja hankalin magoya bayan jam’iyya da jiga-jigan jam’iyyar da kada su kalli sakamakon zaben a matsayin kimar shirinta a babban zabe mai zuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN