Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da sabon Sarkin Birnin Yandoto na karamar hukumar Tsafe ta jihar, Aliyu Garba Marafa, bayan ya yi wa fitaccen kasurgumin shugaban 'yan bindiga, Adamu Aliero sarautar Sarkin Fulani.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wannan na kunshe ne takardar da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya fitar kuma ya bai wa manema labarai a daren Lahadi.
Kamar yadda takardar tace, "Ana sanar da jama'a cewa gwamnatin jihar Zamfara ta baranta kanta saga zagin nadin sarautar Sarkin Fulani wanda Sarkin Birnin 'Yandoton na karamar hukumar Tsafe yayi."
A saboda haka, mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi umarni da dakatar da Sarkin a take.
"Kamar yadda ya dace, gwamnan ya amince da nada kwamiti domin bincikar lamarin da yasa Sarkin yayi wannan aikin.
“A halin yanzu, Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne hakimin 'Yandoto zi cigaba da aiwatar da lamurran sarautar a masarautar."