Wani matashi dan shekara 23 ya kashe budurwarsa har lahira a kan iPhone (Hotuna)


Wani matashi mai shekara 22 da haihuwa ya kashe budurwarsa dalibar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Delta, Ozoro mai suna Gift Oloku saboda wayar salula. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Lamarin ya faru ne a rukunin gidaje na Etevie a Ozoro da ke karamar hukumar Isoko ta Arewa a jihar a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022. 

Wanda ake zargin mai suna Godspower Adegheji, mai shekaru 23, ya yi wa marigayiyar kutse kuma ya sareta da adda har lahira. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce an kama wanda ake zargin.

A cewar Edafe, wanda ake zargin ya kashe Gift ne bayan da ta yi kuskuren karya IPhone dinsa a lokacin da suke fada. 

"Wannan shine Godspower Adegheji na Etevie quarters Ozoro, mai shekaru 23, ya kashe budurwarsa Gift Oloku 'f' mai shekaru 22 a ozoro ta hanyar amfani da adda bayan da ta yi kuskure ta karya IPhone 11pro max din sa yayin da suke fada saboda ta fita ba tare da ta fada masa ba. an kama shi." Kakakin ya bayyana. 

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, an samu matsala ne a daren ranar Asabar din da ta gabata inda wanda ake zargin ya zargi marigayiyar da rashin imani bayan ta fita ba tare da ta fada masa ba kuma fada ya barke a tsakaninsu wanda ya kai ga mutuwar ta. 

Wanda ake zargin ya kai gawar zuwa babban asibitin jihar a safiyar Lahadi inda aka tabbatar da mutuwarta. 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN