Yayin da ake ci gaba da gudanar da zaben Gwamnan jihar Osun ranar Asabar 16 ga watan Yuli, an gan dan gidan Ade "The Dancer" a wani faifen bidiyo yana siyan kuri'u. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Ayoade Ojeniyi ne ya sako bidiyon lamarin a shafinsa na Facebook wanda ke yawatawa yanzu haka a yanar gizo.
Duk da gargadi da jami'an tsaro suka bayar, ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun irin wannan lamari na siyan kuri'u a lokacin zaben na Gwamnan jihar Osun kuma wannan daya ne kawai cikin wadanda ke faruwa a cewar wata majiya.
Latsa kasa ka kalli bidiyo: