Yan bindiga sun yiwa sojoji kwanton bauna a jihar Arewa


Wasu ‘yan bindiga sun yi wa tawagar sojoji kwanton bauna a kauyen Zurak Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

Mazauna yankin sun shaida wa Daily trust cewa ‘yan bindigar sun isa unguwar ne a lokacin da mazauna yankin ke gudanar da harkokin kasuwar.

Manjo Ishaku Takwa, mai magana da yawun rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH) wanda ya tabbatar da harin na kwanton bauna ya ce babu wani soja da aka kashe a lamarin.

Wani mazaunin garin Wase, Abdullahi Usman ya shaidawa jaridar cewa sojoji da ke yankin sun dakile harin.

Kwana daya kafin harin kwantan bauna, ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Pinau na karamar hukumar, inda suka yi awon gaba da shanu sama da 500.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN