An ga jami’an hukumar NDLEA a rumfar zabe na gwamna Gboyega Oyetola da ke Iragbiji, kuma babban birnin karamar hukumar Boripe ta jihar Osun.
Kamar yadda majiyar Legit.ng ta tattaro wadanda ke cikin jihar domin dauko rahotun yadda ake gudanar da zabubbukan gwamna a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli, jami’an NDLEA sun hallara a wajen domin kame masu sayen kuri’u da masu shirin sayar da kuri’unsu.
Kasancewar jami'an tsaro na haifar da tashin hankali a tsakanin wasu mazauna yankin da masu kada kuri'a da tun farko suka dage cewa za su karbi kudi a madadin kuri'unsu, duk kuwa da gargadin da aka yi musu.