Yunkurin tsige Buhari ya yi kamari yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya jefa babbar magana


Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya musanta rahotannin da ke cewa ya na zaune ne kan wasiku daga wasu Sanatoci da suka sanar da shi sauya sheka daga jam’iyyar APC. Shafin isyaku.com ya samo.

Wani rahoto da PM News ya fitar ya nuna cewa Lawan ya musanta rahotannin ta wata sanarwa da Ola Awoniyi mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Rahoton da ya gabata

A halin da ake ciki, rahotanni sun yi ikirarin cewa Lawan na zaune ne a kan wasikun da ake zargin domin kare mukaminsa na shugaban Majalisar Dattawa.

Sai dai wata sanarwa daga ofishin shugaban Majalisar Dattawan ta ce rahotannin karya ne, in ji jaridar New Telegraph.

Da fatan za a karanta cikakken bayanin a kasa:

“Mun ga wani labari a shafukan sada zumunta da wasu jaridun yanar gizo da ke cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan na zaune a kan wasiku daga wasu Sanatoci da ake zargin su da yi masa na ficewa daga Jam’iyyar APC.

“Labarin ya nuna cewa Lawan na zaune ne a kan wasikun da aka ce wai don kare matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa.

“Muna bayyana karara cewa labarin karya ne kwata-kwata domin babu irin wannan wasika da ke gaban Shugaban Majalisar Dattawa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN