IG Model Gena Tew ta ce cutar kanjamau ya sa ta fada ibtila'in rasa motsi da ganinta (bidiyo)


WeWata matashiya mai shekaru 27 da haihuwa a Instagram Gena Tew, wacce ake danganta ta da manyan mashahuran mutane irin su Cif Keef, Chris Brown, da Nick Cannon ta bayyana cewa ta kusa mutuwa daga cutar kanjamau.  Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

A cikin faifan bidiyon da ta watsa, Tew ta ce ba ta san yaushe ko kuma yadda ta kamu da cutar kanjamau ba wanda ya kai ga halin da take ciki.  

Matashiyar mai shekaru 27 ta ce ta yi mamakin lokacin da likitanta ya gaya mata cewa cutar ta kasance a cikin jikinta har tsawon akalla shekaru takwas zuwa goma.  

Likitan ya yi hasashen cewa tabbas ta kamu da cutar kanjamau tun tana matashiya, tsakanin shekaru 17 zuwa 19, bisa ga kima da ya yi.  

Jarumar wanda ba ta tabbatar da cewa tana da kusanci da duk wani mashahuran da aka danganta ta da ita ba, ta ce an gwada ta ne kawai lokacin da alamun suka bayyana.  

Ta kara da cewa, yayin da har yanzu ba ta da tabbacin lokacin da ta kamu da cutar kanjamau, ta kira abokan huldarta domin sanar da su halin da take ciki. Gena ta ce duk wanda ta kira sun ba ta goyon baya sosai, suna duba ta da kuma tabbatar da lafiyarta. Ta ce kawo yanzu, babu wanda ya kamu da cutar bayan sun yi gwaji.

Ta kuma bayyana cewa an yi mata fyade sau da yawa lokacin da ba ta da matsuguni kuma za ta iya kamuwa da cutar tun lokacin da take zaune a kan titunan birnin New York.  

Ma'abuciya TikTok mai shekaru 27 kuma ta ce a baya ta sami yin tattoo kyauta, Kuma ko ta wannan hanyar za ta iya kamuwa da cutar saboda allurar da ake amfani wajen yin tattoo ga kowa zai iya haifar da yaduwar cutar.

A daya daga cikin faifan bidiyo da ta bayyana, ta bayyana cewa nauyinta ya ragu matuka, wanda hakan ya sa ta daina tafiya. Ido d'aya ta makantar da ita kuma sai an yi mata maganin jiki don kawai ta dawo da hayyacin jikinta. 

Kalli bidiyon a kasa...

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN