Wani faifan bidiyo ya nuna wani rago a rufin wani bene mai hawa 2 a jihar Legas, inda ya haifar da manyan tambayoyi kan yadda aka yi har ya isa wurin. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
Bidiyon ya nuna yadda ragon ke yawo a saman rufin a ƙoƙarin neman hanyar tserewa ko hanyar saukowa.
An ce an dauki hoton bidiyon ne a unguwar Ajegunle da ke Legas, amma ba a san mai ragon ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Kalli bidiyo a kasa
Who will help us catch this running ram 🐏?😁 pic.twitter.com/b1VzooAR0Y
— Gboyega Akosile (@gboyegaakosile) July 9, 2022
Rubuta ra ayin ka