Harin gidan yarin Kuje: An kama daya daga cikin yan Boko Haram da suka tsere a jihar Nasarawa


Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kama Hassan Hassan, daya daga cikin wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka tsere daga gidan yarin Kuje a lokacin farmakin da ‘yan kungiyar ISWAP suka kai wa cibiyar a ranar Talata 5 ga watan Yuli.

A ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli ne hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya NCoS ta bayyana sunaye da hotunan fursunoni 69 da suka tsere daga gidan yarin sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai kwanaki uku da suka gabata. 

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ce an kama Hassan ne a Keffi, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce;

“Bayan harin da aka kai gidan kurkukun Kuje da kuma tserewar fursunonin a ranar 9 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 0130 na safe, wani Hassan Hassan ‘M’ wanda sunansa da hotonsa na daga cikin fursunonin da suka tsere bayan jami'an Yan sanda sashen ayyukan sirri suka kama shi a garin Keffi na jihar Nassarawa.


Kwamishinan ‘yan sanda, CP Adesina Soyemi ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa wani wuri mafi aminci yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don neman sauran wadanda suka tsere tare da mika wadanda aka kama.

Kwamishinan ‘yan sandan, ya yaba da kokarin jami’an ‘yan sanda na gudanar da aiki mai kyau, ya kuma ba jama’a tabbacin cewa rundunar na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya ga kowa da kowa.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN