Makashin tsohon Firaministan Japan ya fadi dalili da ya sa ya kashe shi, duba ka gani (Hotunan harin)


Mutumin da ake zargi da kisan tsohon Firaministan Japan Shinzo Abe mai suna Tetsuya Yamagami, ya yi imanin cewa tsohon shugaban na Japan yana da alaka da wata kungiyar addini da ya zargi ya yi sanadin talaucewar mahaifiyarsa sakamakon haka ya shafe watanni yana shirya yadda zai kai harin da bindigar kirar gida, kamar yadda 'yan sanda suka shaida wa kafafen yada labarai na cikin gida a ranar Asabar. Kafar labari na isyaku.com ya samo.

Tetsuya Yamagami, dan shekara 41 mara aikin yi, ya harbe Abe mai shekaru 61 har lahira a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli.

A cikin faifan bidiyon kisan da aka nuna a shafukan sada zumunta, ana iya ganin shi cikin nutsuwa ya tunkari firaministan Japan da ya fi dadewa kan karagar mulki daga baya yana harbe-harbe.

An ga wanda ake zargin yana shiga hanyar daga bayan Abe, wanda ke tsaye a kan wani hawa a wata mahadar, kafin ya yi masa harbi biyu daga wani makami mai tsawon cm 40 (inci 16) nannade da baki tef. ‘Yan sanda sun yi arangama da shi nan take da faruwqr lamarin.


Binciken Yan sanda ya nuna cewa ya yi la'akari da yin amfani da harin bam kafin kafin ya canja ra'ayi ya zabi yin amfani da bindiga, a cewar kafar yada labarai ta NHK.

Wanda ake zargin ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya hada bindigar ne ta hanyar nade bututun karfe tare da tef, wasun su da bututu uku, biyar ko shida, tare da sassan da ya saya ta yanar gizo, in ji NHK.

‘Yan sanda sun gano harsashi a wata alama da ke makale da wata motar yakin neman zabe a kusa da wurin da lamarin ya faru, kuma sun yi imanin cewa sun fito ne daga Yamagami, in ji ‘yan sandan a ranar Asabar. Hotunan bidiyo sun nuna Abe yana juyowa wajen maharin bayan harbin farko kafin a murkushe shi a kasa bayan harbi na biyu.

Ɗaya daga cikin maƙwabcinsa, wata mace mai shekaru 69 da ke zaune a bene a ƙasansa, ta gan shi kwanaki uku kafin kisan Abe


"Na ce sannu amma ya yi biris da ni. Kallon kasa kawai yake yi a gefe bai sanya abin rufe fuska ba. Da alama ya ji tsoro," matar da ta ba sunanta Nakayama kawai, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. "Kamar da alama wani abu ya dame shi."

Kamfanin dillancin labaran reuters ya kuma bayar da rahoton yadda wani mai suna Tetsuya Yamagami ya yi aiki a rundunar kare kai ta ruwa daga shekara ta 2002 zuwa 2005, kakakin rundunar sojin ruwan Japan ya ki bayyana ko wannan shi ne wanda ake zargi da kisan kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN