Yanzu yanzu: An yi wa wani matashi mugun lahani sakamakon duka a garin Bunza jihar Kebbi, duba dalili


Rahotanni da duminsu daga garin Bunza a jihar Kebbi na cewa an yi wa wani matashi miyagun raunuka bayan zargin shiga gidan wani mutum da manufar yin sata. Shafin isyaku.com ya samo.

Bayanai na cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Sambisa a garin na Bunza, da tsakiyar ranar Litinin 25 ga watan Yuli 2022, kuma an aibanta matashin ta hanyar yi masa mumunr lahani a kansa da ya haifar da gudanar jini, ana kuma zargin an sare shi a kafa jijiyar kafarsa ta tsunke.

Anguwar Sambisa a birnin Bunza, ya zama matattarar yawan aikata laifi da barazanar tsaro kamar yadda wata majiya ta ambata, kasancewar Unguwar daga karshen gari kuma ta yi makwabta da dutse da ke malale da babbar daji.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN