Yanzu yanzu: Ma'aikatar ilimi na tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na rufe Kwalejin tarayya na Kwali a birnin tarayya Abuja


Ma'aikatar ilimi na tarayya ta bayar da umarnin gaggauta rufe Kwalejin tarayya ta Gwamnati da ke garin Kwali a babbar Birnin tarayya Abuja. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito.

Ministan ilimi Mallam Adamu ya bayar da umarnin a wata takarda da ta fito daga Daraktan harkokin labarai da hulda da jama'a Mr. Ben Goong ranar Litinin.

NAN ta ruwaito cewa Adamu ya ce rufe Kwalejin ya zama dole sakamakon tabarbarewar tsaro da aka samu a kauyukan Sheda da Lambata da ke makwabta da garin Kwali.

Ya ce yunkurin gaggawa na dauki da jami'an tsaro suka kai na dakile lamarin ya yi matukar tasiri.

Adamu ya bayar da umarnin cewa Makarantu su tsara shiri na musamman yadda daliban ajin karshe za su rubuta jarabawarsu ta NECO.

Ma'aikatar ilimi ta kuma umarci shugabannin makarantun Kwalejin gamayyar hadin kai Unity schools su hada kai da jami'an tsaro a wajen da suke domin samar da tsaro a makarantunsu. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN