Mai mota ya buge Safeton yan sanda da mota, yan sanda sun bindige shi nan take

Mai mota ya buge Safeton yan sanda da mota, yan sanda sun bindige shi nan take


Jami'an rundunar yan sandan jihar Enugu sun bindige wani mutum mai suna Christian Ogwuike bayan ya buge wani Safeton yan sanda da mota a shingen binciken ababen hawa. Shafin isyaku.com ya samo.

Rahotanni sun ce Ogwuike yana tare da budurwarsa a cikin motar  kirar Lexus SUV ranar Alhamis 21 ga watan Yuli 2022, lokacin da Yan sandan suka tsayar da shi a shingen bincike na Shataletalen Monkey Roundabout da ke kusa da ofishin EFCC kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai Kakakin hukumar Yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce mai motar ya buge wani Safeton Yan sanda ne bayan ya ki tsayawa a shingen tsaro na bincike kuma ya ja shi har tafiyar misalin Pol uku, sakamakon haka wani dandanda ya harbe shi a cinya domin hana shi ci gaba da haddasa fitina mai muni.

Ya ce dan sanda da aka buge da mota da shi mai motar da yan sanda suka harbe suna karbar magani a wani Asibiti kuma suna murmurewa.

Rahotanni na cewa tuni Mataimakin kwamishinan Yan sandan jihar sashen binciken manyan laifuka ya jagoranci cikakken bincike kan lamarin bisa umarnin kwamishinan Yan sandan jihar. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN