Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa Sanatan Najeriya daurin shekaru 7 a gidan Yari


Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Legas, a ranar 1 ga watan Yuli ta yanke wa Sanata Peter Nwaoboshi, mai wakiltar Delta North, hukuncin daurin shekaru 7 kan almundahanar kudi.

Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter, kotun ta kuma bada umarnin kwace kamfanoninsa biyu, Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd bisa tanadin sashi na 22 na Money Laundering Act 2021.

Yanke hukuncin ne zuwa ne bayan EFCC ta daukaka kara kan hukuncin da Mai shari'a Chukwuemeka Aneke na Kotun Tarayya Abuja ya yanke a ranar 18 ga watan Yuni 2021 ba wanke wanda ake zargin daga tuhumar da ake masa.

EFCC ta gurfanar da wadanda ake zargin su uku kan zargin mallakar wani kadara mai suna Guinea House, Marine Road, Apapa Lagos kan kudi Naira Miliyan 805.

An yi zargin cewa wani kaso cikin kudin siyan gidan, Naira miliyan 322 da Suiming Electrical Ltd ta tura a madadin Nwaoboshi da Golden Touch Construction Project Ltd kudin ne haramtacce.

Amma, a hukuncinsa, Mai shari'a Aneke ya ce hujja ta PW "ta nuna cewa wanda aka yi ƙarar ya karbo bashin N1.2bn daga wani bankin zamani don siyan karin kayayyaki a matsayin jari.

"Ta kuma nuna cewa bashin N1.2bn tare da ruwa na N24m aka bawa wanda aka yi ƙarar na 3. Bayan haka babu wani abu da mai ƙarar ya tabbatar a Shari'ar," in ji alkalin.

Ya yi ikirarin cewa masu shigar da karar sun gaza kawo shaidu daga bankin domin su taho su kawo wasu takardu na F da F10.

Daga bisani ya wanke tare da sallamar wadanda ake zargin.

Kotun daukaka kara ta canja hukuncin

Amma, a hukuncin yau kan daukaka karar da EFCC ta yi, kotun daukaka karar ta ce alkalin ya yi kuskure wurin watsi da tuhumar da aka yi wa wadanda ake zargi.

Ta ce wanda suka shigar da karar sun gabatar da gamsassun hujjoji da ke nuna an aikata laifin don haka ta kama waɗanda ake zargin da aikata laifi.

A wani rahoton, jami'an Hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annarti EFCC, ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu wurin siyan kuri'u a zaben gwamna na Ekiti.

An kama mutanen da ake zargin ne a wani gida dauke da kudade masu yawa da ake zargin na siyan kuri'u ne zaben kamar yadda ya ke a bidiyon.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN