Type Here to Get Search Results !

Kotu ta yanke wa yan Luwadi 3 hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwatsu a Bauchi ciki har da tsoho mai shekara 70... isyaku.com


Wata kotun shari’ar Musulunci da ke garin Ningi da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi ta yanke hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwatsu kan wasu mutane uku ciki har da wani tsoho dan shekara 70, bayan da ta same su da laifin yin luwadi. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

An bayyana sunayen wadanda aka yankewa hukuncin, Abdullahi Beti (30), Kamilu Ya'u (20) da Mal. Haruna mai shekaru 70, ya fara ne a ranar 14 ga watan Yuni, 2022 bayan da jami’an Hisbah Vanguard da ke aiki a karamar hukumar Ningi ta hannun Adamu Dan Kafi suka kama su. 

Rahotanni sun ce sun amsa laifin da ake tuhumarsu da su. Bayan sauraron bayanan shaidu da kuma amincewa da wadanda ake tuhuma da aikata laifin, Alkalin kotun, Munka’ilu Sabo-Ningi, ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar jifa.

Ya kafa hukuncin ne bisa tanadin sashe na 134 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Bauchi na shekarar 2001 da kuma tanadin Fiquhussunah Jizu’i mai lamba 2 a shafi na 362.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies