Kotu ta dakatar da Gwamnatin jihar Kano daga karbo bashin N10b domin siyo na'urar CCTV.. isyaku.com


A ranar Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman, ta hana gwamnatin jihar Kano rancen naira biliyan 10 domin sanya na’urar daukar hoto ta Closed-Circuit Television (CCTV). Shafin isyaku.com ya samo.

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu, Kano First Forum (KFF) ta shigar da kara mai dauke da kwanan wata 27 ga watan Yuni, wanda Darakta Janar na kungiyar Dakta Yusuf Isyaka-Rabiu ya shigar.

NAN ta ruwaito cewa KFF ta bakin lauyanta, karkashin jagorancin Mista Badamasi Suleiman-Gandu, ta roki kotun da ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano rancen Naira biliyan 10.

Sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Kwamishinan Kudi na Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sauran sun hada da Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar Kula da Kudi.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE