Wata babbara Kotun jihar Kano, ranar Alhamis, ta yanke wa Abdulmalik Tanko da wani mutum daya hukuncin kisa ta hanyar rataye su har sai sun mutu bayan ta kama su da laifin kashe yarinya yar shekara shida mai suna Hanifa Abubakar. Shafin isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa Alkalin Kotun Jastis Usman Na’abba ya kuma yanke wa Fatima Musa hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari.