Da dumi-dumi: Gwamna Bagudu ya rattaba hannu kan wani muhimmin doka a jihar Kebbi



Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya rattaba hannu kan dokar kare hakkin yara ya zama tabbataccen doka. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Bagudu ya kuma rattaba hannu kan kudirin dokar hana cin zarafi ga daidaikun mutane da kuma dokar kare hakkin yara (Dokar kare hakkin yara).

Da yake jawabi bayan sanya hannu a kan kudirin, Gwamnan ya bayyana cewa matakin zai kara nunawa ga kasashen Duniya game da jajircewar Kebbi wajen aiwatar da dokar yaki da cin zarafin mata yadda ya kamata da kuma karfafa kare yara.

“Wadannan dokokin kuma za su karfafa kare yara, duk da cewa wasu daga cikin dokokinmu sun yi tanadin hakan.

"Wannan don ƙarfafa su ne da kuma jawo hankali ga bukatar yin ƙarin," in ji shi.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga Majalisar dokokin jihar Kebbi bisa kwazon da suka yi da jajircewarsu wajen zartar da kudirorin da suka dace da al’adu da addinin al’ummar jihar.

Hakazalika ya yabawa shugabannin addini da sarakunan gargajiya bisa bitar dokar don tabbatar da bin ka’idojin addini.

Bagudu ya nuna godiya ga abokan cigaba da sauran kungiyoyi bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnati wanda ya taimaka wajen aiwatar da doka domin ta fara aiki.

Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga uwargidan sa, Dakta Zainab Shinkafi-Bagudu bisa irin gagarumin goyon bayan da ta bayar tare da kaddamar da wayar da kan jama’a tare da samar da dokar yaki da cin zarafin mata da kuma kare hakkin yara da hakkokinsu.

Gwamnan ya bayyana fatansa cewa dokar za ta yi amfani ga al’ummar jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Majalisar dokokin jihar Kebbi a ranar 5 ga watan Oktoba, 2021 ta amince da kudirin dokar samar da kare hakkin yara a jihar Kebbi da sauran batutuwan da suka shafi.

NAN ta ruwaito cewa jihar Kebbi ita ce jiha ta 30 a Najeriya da ta rattaba hannu kan dokar kare yara ta zama doka

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN