An kama wata karuwa 'yar Najeriya bayan da ta yanke al'aurar wata Karuwa da reza yayin fada


Rundunar ‘yan sandan Ghana a yankin Ashanti ta kama wata karuwa ‘yar Najeriya bisa zarginta da amfani da wuka wajen yanke al’aurar abokiyar aikinta. Shafin isyaku.com ya samo.

Wanda ake zargin wadda aka bayyana a matsayin uwar duk wasu karuwai a Dichemso Plaza ta kuma yi amfani da wukar wajen raunata fuska da cinyoyinta wacce take fada da ita bisa zargin sace daya karuwar ta sace mata kwastoma.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa wacce ake zargin mai suna Bella, ta gargadi abokiyar aikinta, Ruth da ta guji wani mutum saboda mutumin shine babban abokin cinikinta. An kuma tattaro cewa ta yi barazanar za ta “tsara” fuskarta (Ruth) da abubuwa masu kaifi idan ta ƙi bin gargaɗinta. 

Amma bayan da Ruth ta ƙi bin gargaɗin, Bella da wasu mutane huɗu suka bi ta a gefen hanya kuma suka makale ta a ƙasa. Daga baya suka rike hannayenta da kafafunta suka ba Bella damar yanke mata fuskarta da kuma bangarenta.

Mutane hudu da suka taimaka Bella wajen aiwatar da wannan aika aika har yanzu ‘yan sanda ba su kama su ba tun bayan da suka gudu lokacin da suka samu samu labarin kama Bella.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN