Yanzu-yanzu: APC ta zabi Lawan domin maye gurbin abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima a Majalisar Dattawa


Jam’iyyar APC reshen jihar Borno ta zabi babban Lauyan jihar, Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Borno ta tsakiya a karkashin Sen Kashim Shettima, wanda yanzu dan takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam’iyyar. Shafin isyaku.com ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa Jami’in APC kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Taraba, Alhaji Uba Magari, a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar a Maiduguri, ranar Alhamis 14 ga watan Yuli, ya ce tsohon kwamishinan shari’a ya samu kuri’u 459 daga cikin kuri’u 480 masu inganci. Jaridar Sun ta ruwaito.

Ya bayyana cewa:

“Bayan gamsuwa da tanade-tanaden dokar zabe, da hukumar da shugaban mu na kasa ya ba ni, na bayyana cewa Barr. Kaka Shehu Lawan, tsohon Atoni Janar, an zabe shi da inganci a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Borno ta tsakiya na APC. ”

Kaka vs magana

A jawabinsa na godiya, Kaka Lawan ya godewa Gwamnan jihar da wakilan da suka zabe shi.

Ya bukaci wakilan da su tara masu kada kuri’a domin gudanar da rijistar masu kada kuri’a na dindindin.

Lawan ya bayar da tabbacin samun wakilci mai inganci a Majalisar dattawa duk da cewa ya roki jama’a da su rika yi wa shugabanninsu addu’a.

Gwamnan jihar Borno yayi magana

Gwamna Babagana Zulum a nasa jawabin, ya bayyana zaben Kaka Lawan a matsayin ikon Ubangiji, yana mai cewa babu wanda zai iya canza makomar mutum sai Allah.

Ya ce tsohon AG an tsayar da shi takarar ne saboda biyayyar sa ga jam’iyya, tawali’u, sadaukarwa da rikon amana.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN