Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke busasshen ganye wiwi Mai nauyin kg135 wanda darajarsa ta kai N1.3m ana jigilar su a cikin wata mota a karamar hukumar Rogo ta jihar. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 15 ga watan Yuli, 2022, ya ce jami’an tsaro ne suka kama motar a kan iyakar Katsina da Kano bisa samun sahihan bayanan sirri.
PPRO ya ce direban ya bar motar ya tsere bayan ya ga ‘yan sanda. Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike.