Budurwa ta kuwata ta suma bayan magidanci ya shafa laya kafin saduwa da ita


Wani magidanci mai shekaru 33 mai suna Ibrahim Orona da ake zargin ya yi amfani da wata laya wajen saduwa da budurwarsa a ranar Juma’a an tsare shi a gaban wata kotun Majistare da ke Abeokuta. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa Rundunar ‘yan sandan jihar ta gurfanar da Orona, wanda ke zaune a No 35, Ago-oka, unguwar Idi-Oparun a Abeokuta, da laifin yin wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Olakunle Shonibare, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Yuni a unguwar Ago-Ika a Abeokuta.

Shonibare, ya bayyana cewa wanda ake tuhumar ya shafa wani abu (layya) a al’aurarsa kuma ya sadu da budurwarsa mai shekaru 23, Temilade Olabanji.

Ya yi zargin cewa nan da nan bayan gama saduwa da ita sai ta fara ihu kamar kare kuma ta suma.

Mai gabatar da kara ya ce an garzaya da ita wurin wani likitan gargajiya wanda ya farfado da ita kuma daga baya aka garzaya da ita babban asibitin jihar Ogun domin samun kulawar da ta dace.

Ya lura cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 210(c) na dokar laifuka ta Ogun 2006.

Alkalin kotun, Misis OM Somefun, ta bayar da belinsa a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Ta ba da umarnin cewa wadanda za su tsaya masa dole ne su gabatar da shaidar biyan haraji na shekaru uku ga gwamnatin Ogun kuma daya daga cikinsu dole ne ya kasance dan uwa ga wanda ake kara.

Somefun ta ba da umarnin cewa idan wanda ake tuhuma ya gaza cika sharuddan belin, to a tsare shi a cibiyar gyara hali na Oba.

Ta dage sauraron karar har sai ranar 2 ga watan Agusta domin sauraren karar 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN