Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace Shugaba Buhari da Gwamna El-Rufai

Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace Shugaba Buhari da Gwamna El-Rufai


Yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar yin garkuwa da Shugaba Buhari, Gwamna El-Rufai, da sauran su. Shafin isyaku.com ya samo.

DailyTrust ta ruwaito yan ta’addan sun yi wannan barazanar ne a cikin sabon faifan bidiyo da suka fitar da ke nuna yadda suke bulala ga fasinjojin da aka sace.

Idan dai za a iya tunawa a makonnin da suka gabata ne aka kai wa ayarin tawagar shugaban kasa hari a kan hanyarsu ta zuwa mahaifar shugaba Buhari a Daura gabanin Sallah. Mutane biyu sun samu raunuka a harin. Harin da aka kai wa ayarin motocin ya faru ne a ranar da ‘yan ta’addar Daesh a yankin Yammacin Afirka (ISWAP) suka mamaye gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da daukacin ‘yan ta’addan da ake tsare da su.

A cikin sabon faifan bidiyo da ‘yan ta’addan suka fitar, sun yi barazanar cewa matukar gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar wata mahauta.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu. Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi mu sayar da su. 

Kamar yadda ’yan matan Chibok da aka sayar, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi. Idan ba ku biya bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke bukata mu kashe mu sayar da sauran. Da yardar Allah El-Rufai, Buhari za mu kawo ka nan.” Daya daga cikin ‘yan ta’addan da ya yi magana da Hausa ya ce.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN